Wednesday

Home › › kusoshin da ke zagaye da buhari zasu hallaka nigeria


'Kusoshin da ke zagaye da Buhari zasu hallaka Najeriya.

Dakta Junaid Mohammed, yace idan yan Najeriya basuyi hankali ba, kusoshin da ke zagaye da Buhari zasu hallaka Najeriya. Game da cewarsa, abinda yan Najeriya suka gani yanzu na nuna cewa fadar shugaban kasa bata fadawa yan Najeriya gaskiya.

Yace:“Abinda ke faruwa yanzu bai dace ba saboda hujja ya nuna cewa fadar shugaban kasa bata fada mana gaskiya. Suna wasa da hankalin jama’a wadanda suka bata lokacinsu wajen rijistan zabe, yin zaben, har wasu ma suka rasa rayukansu yayin zabe.

Idan majalisar dokoki bata yi motsi wajen tsige shugaban kasan ba, rashawa zata cigaba a wannan gwamnati. Abinda kusoshin da ke zagaye da Buhari keyi shine su shigo da shi, suyi Kaman shine ke shugbantarmu alhalin ba shi bane, kuma idan bamuyi hankali ba, zasu hallaka wannan kasar.”

 
No comments:
Write Comments