Wednesday

Home › › Ma'aikatar harkokin kiwon lafiya ta Jamhuriyar Nijer ta sanar da kawo karshen cutar rift valley a dukkan fadin kasar.




Ma'aikatar harkokin kiwon lafiya ta Jamhuriyar Nijer ta sanar a jiya ranar 14 ga wata cewa, tun daga watan Oktoba na bara zuwa yanzu, babu sabon mutum da ya kamu da cutar zazzabi na Rift Valley a kasar ba, an riga an kawo karshen cutar a dukkan kasar.

Ministan kiwon lafiya na kasar Nijer ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana cewa, tun daga ranar 25 ga watan Oktoba na shekarar 2016, babu sabon mutumin da ya kamu da cutar zazzabi na Rift Valley ba a dukkan kasar.

Bisa ma'aunin kasa da kasa, an riga an kawo karshen cutar a kasar Nijer. Amma ministan ya yi kira ga jama'ar kasar da su yi takatsantsan don magance sake abkuwar cutar a kasar.

A karshen watan Agusta na shekarar 2016, Nijer ta sanar da kawo karshen cutar zazzabi na Rift Valley. Game da wannan batu, kawancen ayyukan likitanci na kasa da kasa da ba na gwamnati ba, ya hada kan hukumomin kiwon lafiya na kasar Nijer, da kafa wata cibiyar ba da jinya a yammacin kasar mafi fama da cutar, wadda ta karbi mutane kimanin 400 masu kamu da cutar.

Bisa kididdigar da aka yi, mutane a kalla 33 sun mutu a sakamakon cutar.









http://fb.com/hausapost28
No comments:
Write Comments