Thursday

Home › › Majalissa zata binciki mataimakin shugaba buhari

  • Majalisar Dattawa za ta binciki
    Mukaddashin shugaban kasa Yemi
    Osinbajo.
  • Majalisar za ta gudanar da bincike a game da Gidan Mataimakin shugaban
    kasar.
  • Sanata Dino Melaye ne zai yi wannan aiki

Majalisar Dattawa za ta gudanar da
wani bincike a game da gidan zaman
Mataimakin shugaban kasa wanda
shine Mukaddashin Shugaban kasa a
yanzu haka. Majalisar na zargi an tafka
badakala wajen gina gidan Mataimakin
shugaban kasar.


Jaridar Punch tace da alamu dai
Majalisar Dattawa za ta gudanar da
wani bincike a game da ginin da ake yi
na gidan mai girma Mataimakin
shugaban kasa Yemi Osinbajo a cikin
Birnin-Tarayya Abuja.

Sanata Dino Melaye wanda shine
shugaban kwamitin kula da Birnin
Tarayya a Majalisar yace kudin da aka
ware har Miliyan N250 na ginin gidan
Osinbajo yayi yawa. Sanata Melaye ya
kuma ce an tsula kudi wajen ginin
gidan Shugabannin Majalisar Kasar.
Kwanan nan aka gano dai cewa an buga
cuwa-cuwa wajen harkar gidajen
Shugabannin Majalisar da Mataimakan
su. Sai dai Shugaban Majalisar Dattawa
Sanata Bukola Saraki ya karyata hakan.


A biyo mu a shafin mu @fb.com/hausapost28
No comments:
Write Comments