Friday

Home › › Masanan Kimiyya sun gano nahiya ta 8 a karkashin tekun Oceanic.

Masanan Kimiyya sun bayyana gano wata sabuwar nahiya a karkashin tekun Oceanic da ke yankin Pasific wada suka ce za ta iya zama nahiya ta 8 a duniya.Masanan Kimiyya sun bayyana gano wata sabuwar nahiya a karkashin tekun Oceanic da ke yankin Pasific wada suka ce za ta iya zama nahiya ta 8 a duniya.

An buga binciken masanan a mujallar "Geological Society of America's Journal" inda a jawabin da aka yi aka ce, sun gano nahiyar wadda kaso 94 nata ya ke cikin tekun kudu maso yammacin Pasific kuma tana da girman kilomita miliyan 5 wato ta kai 1 bisa ukun nahiyar Ostireliya.

Daya daga cikin marubutan kimiyya dan kasar Niyu Zelan Nick Mortimer ya ce, masanan sun yi aiki na kusan shekaru 20 don gano nahiyar da ake kira "Zelanda".


@hausapost28 on Twitter
No comments:
Write Comments