Monday

Home › › MAUDU'I AKAN RASHIN LAFIYAR BUHARI | AREWA TANA CIKIN GARARI


Jiya Lahadi a lokacin da 'yan Arewa suka samu
Shugaba Muhammadu Buhari, wacce ya aiko wa
Majalisa cewa zai qara adadin kwanakin jinyarsa
a Ingila, jama'a da dama sun shiga cikin damuwa
da firgicin rashin sanin makoma. Saboda a
sannan ne ta fara bayyana cewa qila fa a sake
maimaita abin da ya faru a zamanin Umaru
'Yar'aduwa.
Wannan tunani ya qara samun gindin zama a
zukatansu ne ganin cewa shugaban bai fadi
yaushe ne ma zai dawo ba. Sannan ga kuma
binciken kafar yad'a labarai ta Saharareporters
ya nuna Buhari yana buqatar ya ci gaba da
zaman jinyarsa har nan da watanni hud'u masu
zuwa. Kafar ta ce wata majiyarta daga fadar
shugaban qasa ta fallasa mata cewa Buhari yana
buqatar tiyatar da za ta tilasta shi barin aiki har
na aqalla tsawon watanni hud'u, amma
muqarrabansa ba sa son ya kai wannan tsawon
lokaci don gudun rasa tasiri a fawa.
Jaridar Vanguard ta marecen jiya Lahadi (ta
yanar gizo), ta zaqulo bayanin irin cutar da ke
damun Shugaba Buhari. Jaridar ta ce cutar
mummuna ce kuma ba ta da magani.
Wannan yana nuni ne da samuwar wata matsala
babba ga Arewa.
Kafin wannan lokaci, kimanin mako guda baya,
kwatsam sai ga jaridun Nijeriya sun ruwaito
tsohon shugaban qasa Cif Olusegun Obasanjo
yana da'awar dacewar hannanta mulki ga 'yan
qabilar Ibo a shekarar 2019. Duk da cewa
akasarin su 'yan qabilar ta Ibo sun watsa masa
qasa a ido kan wannan zuma da ya lasa mu su a
baki, hakan dai bai nuna babu wani lauje cikin
nad'in siyasar Buharin ba. Domin me zai sa
Obasanjo ya yi wannan da'awa a rana tsaka
alhali tsawon lokaci yana yabon salon
shugabancin Buharin?
Kazalika a ranar Jumu'ar da ta gabata sai kuma
aka sake jinsa yana shaida wa duniya cewa:
"wad'anda suke fatan Buhari ya mutu mugaye
ne."
Shi ma wannan, yana nuni ne da samuwar wata
matsala 'boyayya ga Arewa.
A makon farko da Buhari ya bar qasar nan, ba a
d'au lokaci ba fadar shugaban qasa ta saki
takardar manema labarai tana qaryata tsegumin
da ke yawo a cikin qasa cewa an nemi
Mataimakin Shugaban qasa Yemi Osinbajo ya yi
murabus daga muqaminsa. Fadar ta ce tsegumin
qarya ne tsagwaro. Babu samuwarsa. Shin abin
da babu shi, me ya kawo maganarsa?
Shi ma wannan yana nuni ne ga qoqarin da wasu
ke yi na tsirar da sabuwar matsala a tsakanin
Arewa da wasu yankunan qasar nan.
Idan aka gwama duk wad'annan a wuri guda, za
a iya sunsunar ababe uku a lissafin siyasar
kutungwila, murd'iya da babakere.

 • 1. Akwai yiwuwar rashin lafiyar nan na Buhari ba
  qanqane ba ne, qila ma na ajali ne. Kuma da
  alamu wasu sun san haka.

 • 2. Akwai wani yunquri na had'a Arewa fad'a da
  sauran yankunan qasar nan kan batun wanda zai
  gaji Buharin idan ya mutu ko kuma wa'adinsa ya
  cika.

 • 3. Al'ummar Arewa a gafale suke, saboda sun
  shagalta kansu da rikicin wane ne musulmin
  qwarai, wane ne ba na qwarai ba, kishiyoyinsu
  kuma suna can sun yi nutso cikin shirya wa
  yankin kutugwila ta hanyar tad'iye qafafun
  'ya'yan yankin kan sha'anin shugabancin qasa.
  Bisa ga wannan nazarin hasashe nake tuna
  waqen Marigayi Sa'adu Zungur a inda yake cewa:
  "Komai na Arewa da bambamci da na al'ummomi
  sun fi d'ari.

 • "Daularsu daban, cinikinsu daban, iliminsu daban
  don ba nazari.
  "Daularsu kamar rigarsu take, ga yawa ba amfani
  na gari.
  "Cinikinsu kamar wandonsu yake, bujensu da ba
  shi da alkadari.
  "Iliminsu kamar rawaninsu yake, d'aure-d'auren
  banza ba nazari."
  Allah ya jishe mu alheri!


  kasance damu a@fb.com/HAUSAPOST28
  No comments:
  Write Comments