Monday

Home › › Mr Trump ya Fadi dalilin dakatar da musulmi daga shiga amurka
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce shirin rage yawan mutanen da ke shiga Amurka daga kasashen musulmi ya zama wajibi saboda yadda duniya ke cikin rikici.

Trump ya shaidawa kafar yada labaran ABC cewa ba yana nufin dukkanin musulmi zai haramtawa shiga Amurka ba illa ‘yan kasashen da ke fama da rikici.
Sai dai shugaban bai fadi kasashen da ya ke nufi ba, amma ya taba cewa kasashen Turai sun tabka babban kuskure musamman Jamus da ta amince ta karbi dubban ‘yan gudun hijira.
Rahotanni daga Amurka sun ce shugaba Donald Trump zai haramtawa mutanen Syria shiga kasar, sannan za a dakatar da bayar da biza ga mutanen kasashen Iraqi da Sudan da Somalia da Libya da Yemen.
Gwamnatin Trump kuma na shirin datse yawan ‘Yan gudun hijira 100,000 da gwamnatin Obama ta yi alkawalin karba zuwa dubu hamsin.
Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama ta Human Rights Watch ta ce ya zama dole ga sauran kasashen duniya su tashi tsaye wajen kare hakkokin duniya saboda yadda shugaban Amurka Donald Trump ke neman sauya matsayin kasar.
Daraktan kungiyar Kenneth Roth ya bayyana damuwarsa cewar kungiyar za ta rasa matsayin Amurka na kare hakkoki a fadin duniya, inda ya ke cewar hakan zai taimaka wajen karuwar cin zarafin jama’a.
Roth ya ce wasu kasashen duniya za su yi amfani da sabon matsayin Amurka wajen taka hakkokin jama’a.
Tun rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban Amurka na 45, ya fara aiwatar da alkawullan da ya sha fada a yakin neman zaben shi.
Shugaban ya bada umurnin fara aikin gina Katangar da za ta raba Amurka da Mexico, matakin da ya harzuka shugaba Enrique Pena Nieto da sauran shugabannin Yankin.
Trump ya bukaci jami’an sa da su tsara yadda za’a fara ginin, inda yake cewa daga yau Amurka ta kama hanyar kare iyakokinta.

fadi ra'ayin ka a @HAUSAPOST28/RA'AYOYI
No comments:
Write Comments