Saturday

Home "Mun gode Allah da ka bamu Osinbanjo" - Na hannun daman Jonathan


Tsohon mai taimakawa tsohon shugaba
Jonathan a kan sabbin hanyoyin sadarwa,
Reno Omokri ya yabawa mukaddashin
shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo bisa
sallamar wasu daraktoci guda 9 a hukumar
kula da sufurin jiragen sama (NCCA).

A kuma wasu jerin sakonnin Tuwita kuma,
Omokri ya yi izgili ga manufofin shugaba
Buhari wadanda ya ce, ba su taimaki 'yan
Najeriya ba kamar na Osinbajo, wanda ya
hau ragamar iko a 'yan makwanni kadan.Tsohon mai taimaka wa tsohon shugaba
Jonathan a kan sabbin hanyoyin
sadarwa, Reno Omokri ya yabawa
mukaddashin shugaban kasa Farfesa
Yemi Osinbajo bisa sallamar wasu
daraktoci guda 9 a hukumar kula da
sufurin jiragen sama (NCCA).
Omokri ya gamsu da kwazon Osinbajo
bayan da Osinbanjon ya sallamar
daraktocin su 9 bayan kai wata ziyarar
ba-za-ta da ya kai filin,


A wani sako daya lika a shafinsa na
dandali sadarwa na sada zumunta da
muhawara na Tuwita, a yammacin
ranar Juma'a 24 ga watan Fabrairu,
Omokri ya yabawa Osinbajo bisa
matakin gaggawa da ya dauka na
sallamar daraktocin bayan ziyarar ba-
za-ta da ya kai filin saukar jiragen
sama na kasa da kasa na Murtala
Muhammad da ke Legas ranar Alhamis
23 ga watan Fabrairu.
Omokri ya ce, hukuncin na Osinbajo a
kan daraktocin a sa'oi 24 bayan ziyarar
misali ne na kyakkyawan shugabanci.

Sannan ya kuma ce:

"Mukaddashin shugaban kasa Farfesa
Yemi Osinbajo ya kai ziyara filin saukar
jiragen sama na Murtala Muhammad,
kuma bai ji dadin yanayin da ya samu
bandakunan a ciki ba. Washegari ya
sallami duk wasu daraktoci na hukumar
kula da sufurin jiragen sama ta kasa".
"Wannan shi ne shugaba!" A cewarsa.
"Ba ruwansa da kwarzanta rundunar
sojin kasa, ko kuma tura wa mutane
EFCC. Ba ya surutu. Ba ya dorawa
gwamnatocin baya laifi. Aikinsa kawai
ya ke yi, kuma aikin da ya ke a nutse ya
girgiza Najeriya."

Omokri ya kuma ce, " Ma'aikatu da
kuma wasu sassan wasu hukumomin
gwamnati su na ganin sakamakon aikin.
Mun godewa Allah da ka ba mu
Osinbajo!"


A kuma wasu jerin sakonnin Tuwita
kuma, Omokri ya yi izgili ga manufofin
shugaba Buhari wadanda ya ce, ba su
taimaki 'yan Najeriya ba kamar na
Osinbajo, wanda ya hau ragamar iko a
'yan makwanni kadan.

In za a tunawa dai Osinbajo ya ziyarci
filin saukar jiragen sama na Legas a
ranar Alhamis, ya kuma duba wasu
kayayyakin amfani da su ka hada da
bandakuna da injin daukar jaka.
No comments:
Write Comments