VISIT US ON AREWASOUND.COM


HOTTREND ONLINE :
Music Mp3 - Sabuwar Wakar Hamisu Breaker mai suna - Bazana Manta Maryam Ba.
CHECK NEW PRODUCTS HERE
Hamisu breaker 2020 Album Download Mp3 music

Sammani aa 2020 Album : Download Complete Album (Akwai lokaci)

Umar M Shareef Zeenaru 2020 Official AUDIO+VIDEO

MUSIC: Melery 2020 Song Da Dadi So

Saturday

Home › › Mutane 17 sun mutu a filin kwallo : Angola.


Ma'aikatar 'yan sandan kasar Angola ta ce turereniya da ta afku a filin kwallon kafa na birnin Uige da ke arewacin kasar a lokacin da masu sha'awar kwallon kafa suka nemi shiga filin ta yi sanadin rasuwar mutane. Filin kwallon dai mai daukar mutun 12,000 ya cika makil a daidai lokacin da daruruwan masu sha'awar kallon kwallon suka nemi shiga da karfi.

Shugaban kungiyar kwallo kafa ta Santa Rita ya dora alhakin hakan kan jami'an tsaro da suka bari har mutanen suka iso kusa da kofar shiga duk kuwa da cewa filin kwallon ya cika makil. An dai sha samun irin wannan hadari a filayen kwallo sakamakon turereniya, inda a shekarar ta 2001 mutanen 127 suka mutu a filin kwallon kafa na Accra a kasar Ghana, yayin da 2009 irin haka ta faru a birnin Abija na kasar Cote d'Ivoir, inda mutane 19 suka rasu a wani wasa da kasar ta buga da Malawi.


Facebook/HAUSAPOST28
No comments:
Write Comments