Friday

Home › › Mutane 47 aka kashe a harin bam a Baghdad.
Mutane 47 ne suka mutu inda wasu 50 suka samu raunuka sakamakon harin bam da aka kai da wata mota dauke da bama-bamai a baghdad babban birnin kasar Iraki.

Mutane 47 ne suka mutu inda wasu 50 suka samu raunuka sakamakon harin bam da aka kai da wata mota dauke da bama-bamai a baghdad babban birnin kasar Iraki. An kai harin ne a tashar mota ta Al-Bayya wadda fararen hula suke harkoki a ciki.

Kungiyar ta'adda ta Daesh ta dauki alhakin kai harin. A yankin Al-Sadr da ke gabashin Baghdad an kai wani harin a wajen gyaran mota inda aka kashe mutane 12 tare da jikkata wasu 30. Turkiyya ta la'anci wadannan hare-hare da aka kai a Baghdad.

Ma'aikatar Harkokin Wajen kasar ta fitar da sanarwa cewa, suna tare da 'yar uwarsu kasar Iraki a irin wannan mummunan lokaci da ta shiga kuma zasu ci gaba da hada kai don yaki da ta'addanci. Amurka ma ta fitar da sanarwa inda ta soki harin tare da mika ta'aziyya ga iyalan wadanda aka kashe.@hausapost28 on Twitter
No comments:
Write Comments