Friday

Home › › Nigeria Ta Kara gaba zuwa mataki na 41 A jadawalin hukumar Fifa

Kungiyar kwallon kafar Najeriya ta daga da matakai tara zuwa gaba, a jerin jadawalin hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, inda ta kai mataki na 41 daga na 50 da take a cikin watan da ya gabata.

Jadawalin na watan Fabreru, da hukumar FIFA ta wallafa a shafinta na Website, ya nuna cewa, har yanzu Najeriya na rike da matsayinta na 7 a nahiyar Afrika, duk da gazawarta na shiga gasar cin kofin Afrika da aka kammala a ranar Lahadi da ta gabata, da Kungiyar kwallon kafar Kamaru, Indomitable Lions ta lashe. Sabon jadawalin na FIFA ya nuna cewa, Kungiyar Super Eagles ta Najeriya ta samu maki dari shida da tamanin da shida, wanda ya dara maki dari shida da goma sha tara da ta samu a watan Junairu.


@facebook/HAUSAPOST28
No comments:
Write Comments