Wednesday

Home › › Osinbajo ya ki sanya hannu a kan wasu dokoki hudu a Najeriya.


Mukaddashin Shugaban Kasar Najeriya Yemi Osinbajo.


Mukaddashin shugaban Najeriya Yemi Osibanjo yaki sanya hannu kan wasu dokoki guda hudu da Majalisar kasar ta amince da su.

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya bayyana haka a wasikar da Osinbajo ya rubutawa Majalisar.

Osinbajo ya bayyana dalilan da ya sa dole a yiwa dokokin gyara.

Dan Majalisa Dino Melaye daga Jihar Kogi ya bayyana bacin ran sa da matakin inda ya ce bangaren zartarwa na da damar zuwa kotu idan bata gamsu da dokar ba.

Shugaban Majalisar ya ce za su nemi shawarar bangaren Shari'a a kai.


hausapost28 on Facebook
No comments:
Write Comments