Friday

Home › › PDP ZA TAYI MAJA DA JAM"IYYU 7 KAFIN ZABEN 2019
Jam’iyyar PDP ta ce za ta yi maja da wadansu jam’iyyu bakwai kafin tunkaran zaben 2019.


Tsohon ministan watsa labarai Jerry Gana ne ya sanar da hakan lokacin da yake mika rahoton kwamitinsa da uwar jam’iyyar ta nafa domin bata shawarwari akan hanyoyin da za ta bi domin warware matsalolin da ta ke fama da su yanzu. PDP tace zata hade da jam'iyyu 7 kafin zabe Jery Gana yace jam’iyyar na tattaunawa da wadansu jam’iyyu a kasa Najeriya domin yin maja kafin zaben 2019.


Tsohon ministan ya ce yana da tabbacin cewa jam’iyar APC ba za ta kai labari ba a zaben 2019 musamman ganin irin shirin da jam’iyyarsa ta ke yi domin tunkarar 2019. Ya kuma karyata jita jitan da ake ta yada wa wai jam’iyar PDP za ta canza suna bayan tayi maja da wadansu jam’iyyu .


Jerry Gana yace jam’iyyar PDP ba za ta canza sunanta ba.
©facebook/HAUSAPOST28

A wani RAHOTON kuma :::--- Gwamnatin Najeriya ta ce ta karbe ikon kamfanin jiragen sama na Arik wanda ke fama da bashi mai dumbin yawa da ke neman durkusar da kamfanin. An kwashe tsawon lokaci kamfanin Arik, wanda ke daukar nauyin kashi 55 cikin 100 na matafiya a kasar, yana fama da kalubale da dama. Kamfanin yana ta fuskantar tangarda sakamakon rashin kyakkyawan shugabanci da matsaloli wajen gudanar da ayyukansa da rashin biyan ma'aikatansa albashi da kuma dumbin bashi da ake bin sa. Wadannan matsaloli ne suka sa hukumomin kasar suka shiga tsakani domin shawo kan al'amarin saboda kar kamfanin ya rushe.©facebook/HAUSAPOST28

No comments:
Write Comments