Tuesday

Home Rikici Ya Barke tsakanin "Yan majalissun Dokoki Akan Lafiyar shugaba Buhari.
Toh fa! Rikici ya kunno kai a
majalisar wakilai kan lafiyar
shugaba Buhari.
A yau Talata 28 ga watan Feburairu ne
wata rikici ta kunno kai zaman majalisar
wakilan dokokin kasra nan inda kalmar
‘rashin lafiya’ da wani ya danganta ma
shugaban kasa Muhammadu Buhari ta
janyo cec kuce.


Jaridar Punch ta ruwaito yan majalisun
sun yi cacar baki a tsakaninsu kan
lamarin tafiyar shugaban kasa kasra
Birtaniya don duba lafiyarsa.
Rikicin ya samo asali ne yayin da
shugaban masu rinjaye na majalisar
wakilan Femi Gbajabiamila yayi
gargadin abokin aikinsa kuma bulaliyar
majalisa Alhassan Ado Doguwa daga
amfani da kalmar ‘mara lafiya’ wajen
siffanta shugaban kasa.
Gbajabiamila ya dage kan lallai shugaba
Buhari yaje duba lafiyarsa ba wai ba shi
da lafiya bane, inda shi kuma Doguwa
yace shugaba Buhari bashi da lafiya ne,
don haka ya tafi neman lafiya a kasar
Birtaniya. Sai dai dukkanin yan
majalisun yan jam’iyyar APC ne, inda
Femi ya fito daga jihar Legas, shi kuma
daga Kano.

Doguwa yayi wannan batu ne yayin
dayake jawabi kan karar da aka kawo
bainar majalisar na cewa an ci
mutuncin magoya bayan tsohon
gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa
Kwankwaso, wato yayan
Kwankwasiyya, da wani dan majalisan
daga jihar Kano Aliyu Madaki ya kawo.
Doguwa ya bayyana zargin a matsayin
zance mara tushe balle madafa, inda
yace ai yan Kwankwasiyya ne ke yawo
kwararo kwararo suna ingiza jama’a
garin Kano don suyi ma gwamnatin
Ganduje bore.

Ado Doguwa yace a wannan halin da
kasar ke ciki na dar dar sakamakon
tafiyar shugaban kasa, bai kamata ace
wasu kungiyoyin siyasa na yin abin da
zai iya tada hankula ba, inda ya kara da
cewa kungiyar kwakwasiyya ta fara ma
madugunta yakin neman zaben
shugaban kasa a 2019.

Shugaban kasar mu bashi da lafiya a
kasar waje, irn wadannan harkokin
siyasan basu dace ba a yanzu, don haka
dole ne yansanda su yi aikinsu na
tabbatar da zaman lafiya.” Sai dai
wannan kalma da Doguwa yayi amfani
da ita bata yi ma Femi Gbajabiamila
dadi ba, inda nan take yayi masa raddi.
Tun a 19 ga watan Janairu ne shugaba
Buhari ya tafi kasar Birtaniya da niyyar
zai dawo 6 ga watan Feburairu, don
haka ne ya mika ma mataimakinsa
ragamar mulki.

Amma a ranar 5 ga
watan Feburairu ne shugaban ya aiko
da wata takarda dayake cewa zai
tsawaita hutun nasa har sai an
kammala wasu gwaje gwaje
Hakan ya sanya yan Najeriya cikin
damuwa da dimuwa, amma da manyan
mutane suka fara kai masa ziyara, an
gagga hotunansa kuma yana cikin
koshin lafiya, hakan ne ya kwanar da
hankulan yan kasa.
No comments:
Write Comments