Monday

Home Sanata Kwankwaso ya samu lambar yabo a kasar Afrika ta kudu.
Mujallar African Leadership Margazine
(ALM) dake birnin Landan ta baiwa sanata
Rabi'u Musa Kwankwaso lambar yabo na
gwarzon shekara.GWARZO: Sanata Kwankwazo ya samu lambar
yabo a kasar Afrika ta kudu
Tsohon gwamnan na jihar Kano ya
samu wannan lambar yabon ne bisa ga
gudummawar da ya bayar a fannonin
ilmi da ci gaban al'umma a lokacin da
yake gwamna a tsakanin shekara 2011
zuwa 2015, kamar yadda shugaban
kwamitin amintattu na mujallar,
Ambasada Joe Beasley ya bayyana.
An gudanar da taron ne a Johannesburg
babban birnin Afrika ta Kudu.

Wasu daga cikin wadanda aka baiwa
lambar yabon a baya sun hada da
tsohon shugaban kasar Ghana, John
Mahama; uwargidan shugaban kasar
Afrika ta Kudu, Bongi Ngema-Zuma;
matashin biloniyan nan na kasar
Tanzania , Mohammed Dewyi da
sauransu.

Sai kuma Dakta Mo Ibrahim, shugaba
Ellen Johnson-Sirleaf ta kasar Liberia da
shugaba Jakada Kikwete na kasar
Tanzania.
No comments:
Write Comments