Friday

Home SHEKAU YA KASHE KAKAKINSA :RIKICIN SHUGABANCIN BOKO HARAM
Rikicin shugabanci sakanin Boko
Haram:

Rashin jituwa sakanin shugabanin
kungiyar ‘yan ta’adda Boko Haram ya
sanadiyar kisan kakakin shugaban,
Abubakar Shekau.Ainihin shugaban Boko Haram,
Abubakar Shekau, ya amince da kisan
kakakin bangaren kungiyar kan wani
makirci hambarar da shi, ya ce a cikin
wata sautin rikodi wadda aka samu ta
hanyar AFP.

A cikin sautin na minti 50 a wani taro
da sauran ‘yan kungiyar, Shekau ya ce
ya kashe "Tasiu" wanda aka sani da Abu
Zinnira, wanda kuma ya fito da dama a
wasu bidiyon saƙonnin kungiyar.
Ya ce: "Ya kamata ku ji ni da kyau, na
kashe Tasiu"
ya gaya wa taron da
harshen Hausa wadda shi ne yaren da
ake amfani a fadin arewa maso
gabashin Najeriya.

Shekau ya bayyana ranar da aka
gudanar da taron, 18 ga watan
Disamba, 2017, ya ce ya kira taron
domin tattauna a kan wadanda suke
gunaguni a kan kisan Tasiu.
AFP ya samu kwafi na rikodi a farkon
wannan watan. Kaset wadda aka raba
sakanin ‘yan kungiyar .


hausapost28 on Facebook
No comments:
Write Comments