Saturday

Home shugaban Amirka trump ya sake bayyana aniyar sa ta korar baki

Shugaban Amirka Donald Trump ya sake bayyana aniyarsa ta korar baki daga kasar.


Shugaban Amirka Donald Trump.

Shugaban kasar Amirka Donald Trump ya sake bayyana aniyarsa ta korar baki daga Amirka, musamman wadanda aka samu da aikata manyan laifuka.

A wani jawabin da ya gabatar gaban taron maso ra'ayin 'yan mazan jiya a wannan Juma'ar, Mr. Trump ya ce tuni ma jami'an shige da ficen kasar suka fara aikin binciken dillalan muggan kwayoyi da sauran laifuka don gano su daga duk inda suke a kasar.

Bayanan Shugaban na Amirka dai na zuwa ne rana guda bayan sakatarn tsaron kasar ya yi wasu kalamai da suka bambanta da wannan kan abin da ya shafi fitar da baki daga Amirkar. Sakataren tsaron kasar John Kelly ya fada a kasar Mexico cewar Amirka ba za ta yi amfani da karfi ba wajen tasa keyar baki, bayanan kuma da Shugaba Donald Trump ya warware a jiya.
No comments:
Write Comments