VISIT US ON AREWASOUND.COM


HOTTREND ONLINE :
Music Mp3 - Sabuwar Wakar Hamisu Breaker mai suna - Bazana Manta Maryam Ba.
CHECK NEW PRODUCTS HERE
Hamisu breaker 2020 Album Download Mp3 music

Sammani aa 2020 Album : Download Complete Album (Akwai lokaci)

Umar M Shareef Zeenaru 2020 Official AUDIO+VIDEO

MUSIC: Melery 2020 Song Da Dadi So

Saturday

Home › › Shugaban Amurka Donal trump yã caccaki "yan Jarida.
Donal trump yayin DA suku kace-nace DA wani Dan jarida

Shugaban Amurka Donald Trump ya soki kafafen yada labarai da kakkausan harshe dangane da rahotannin da suke yayatawa na alakarsa da kasar Rasha da kuma shafa wa himmarsa ta dawo da martabar Amurka bakin fenti.

Donald Trump ya bayyana hakan ne a yayin jawabi ga taron manema labarai da ya kira a Washington.

Trump ya kuma koda nasarorin da ya ce gwamnatinsa ta samu a bangaren farfado da karsashin kasuwar hada-hadar hannun jarin kasar, da kuma kamen bakin haure da ba su da takardun izinin zama a Amurka.

A cikin jawabin da ya gabatar yayin taron manema labaran tsawon mituna 76 Trump ya ce abin takaici ne ganin yadda rashin gaskiyar kafafen yada labaran ya wuce kima. Donald Trump ya kuma zargi kafafen yada labarai musamman na kasar da yi wa wasu ‘yan tsiraru aiki.

Wannan dai ba shi ba ne karon farko da Trump ke sukar 'yan jarida ko shiga sai-in-sa da su tun bayan da ya soma jan ragamar mulkin Amurka.


HAUSAPOST28 in Facebook
No comments:
Write Comments