Thursday

Home › › Shugabannin majalissun tarayya Sun Gãna da shugaba Buhari.
Shugabannin Majalisar Tarayyar Najeriya Senata Bukola Saraki da Hon Yakubu Dogara sun gana da shugaba Muhammadu Buhari a wata ziyara ta musamman da suka kai London inda ya ke gudanar da hutu.

AKWAI HOTUNA A 'KASAHotunan da fadar gwamnatin Najeriya ta wallafa a Intanet ya tabbatar da shugaban na cikin koshin lafiya inda ya ke zaune yana dariya tare da Shugaban Majalisar Dattijai Senata Bukola Saraki da Kuma Kakakin Majalisar Wakilai Hon Yakubu Dogara.

A jiya Laraba ne shugabannin Majalisar Tarayyar suka tafi London domin ganawa da shugaba Buhari bayan ya shafe makwanni yana hutun rashin lafiya. Babban mataimaki na musamman ga shugaban na Najeriya kan harkokin majalisar wakilai Abdurrahman Kawu Sumaila ya shaidawa RFI Hausa cewa ziyara ce kawai ta musamman shugabannin Majalisar suka kai wa Buhari a London. Amma a cewar Hon Sumaila, ziyarar ta kunshi tattaunawa da shugaban kan sha’anin Najeriya duk da abubuwa na tafiya ba matsala tare mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbanjo. “Ba daidai ba ne ya dade ba tare da shugabannin Majalisar sun tattauna da shi ba” in ji Hon Kawu Sumaila.

Batun rashin lafiyar Buhari dai ya canjo cece-kuce bayan ya tsawaita wa’adin hutun da ya dauka na kwanaki 10 inda Wasu ‘Yan kasar ke ganin tsawaita hutun ya tabbatar da shugaban ba ya cikin koshin lafiya. Amma Kakakinsa Malam Garba shehu ya ce Buhari na shirye shiryen dawo wa gida Najeriya yanzu haka ‘Yan Najeriya dai sun kagu shugaban ya dawo, domin tabbatar da koshin lafiyarsa.

HOTUNA

kasance damu a twitter @hausapost28
No comments:
Write Comments