Friday

Home › › Sojin Najeriya sun yi ruwan bama-bamai kan wasu ‘yan ta’aaddar Boko Haram.

Sojojin saman Najeriya sun yi ruwan bama-bamai kan ‘yan ta’addar Boko Haram tare da kashe wasunsu a yankin arewa maso-gabas bayan da ‘yan ta’addar suka yi harbi kan jirgin saman sojin da ke aiyukan kai dauki ga marasa lafiya.

Kakakin rundunar sojan saman kasar Gurup Kaftin Ayodele Famuyiwa ya bayyana cewa, jami’ansu na cikin jirgin mai saukar ungulu don kai kayan kula da lafiya zuwa Gwoza wanda a kan hanyarsa ‘yan ta’addar Boko Haram suka nemi kai masa hari. ‘Yan ta’addar sun yi harbi kan jirgin saman samfurin Mi-17 inda harsashi ya sami wani jami’i 1.

Bayan kai harin ne rundunar sojin ta aike da jirgin yaki zuwan yankin da lamarin ya faru wanda ke tsakanin Bama da Gwoza, kuma an samu nasarar kashe ‘yan ta’addar na Boko Hara da dama.@hausapost28 on Facebook
No comments:
Write Comments