Friday

Home › › Sojojin Najeriya 8 sun mutu a harin Boko Haram.
Sojojin Najeriya 8 sun mutu a harin kwanton bauna da mayakan Boko Haram suka kai musu. REUTERS/Tim Cocks

Akalla Sojojin Najeriya 8 ne suka mutu a wani harin kwanton bauna da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai musu kamar yadda majiyar tsaro a kasar ta sanar.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya rawaito cewar an kai wa sojojin harin ne da safiyar yau juma’a a kauyen Ajirin da ke yankin Mafa mai tazarar kilomita 50 a gabashin birnin Maiduguri da ke jahar Borno. Majiyar sojin kasar ta kuma ce akwai wasu sojoji biyu da suka sami rauni a musayar wutar da aka yi da mayakan na Boko Haram. Wani shedun gani da ido ya ce harin kwanton bauna mayakan suka kai kan sojojin a yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Dikwa, al’amarin da ya sa aka sami asarar rayukan sojojin da yawa.

Ruundunar sojin Najeriya da gwamnatin kasar sun sha cewa sun karya lagon kungiyar yayin da wani sabon rahoto na Majalisar Dinkin Duniya ma ke cewa kungiyar ta riga ta talauce. Mutane fiye da dubu ashirin ne suka mutu tun bayan da kungiyar Boko Haram ta soma kai hare-hare da sunan fafutukar kafa daular musulunci a Najeriya.
©facebook/HAUSAPOST28
No comments:
Write Comments