Sunday

Home › › Steinmeier ya zama sabon shugaban kasar Jamus

'Yan majalisun Tarayyar da na jihohi a nan Jamus, sun zabi tsohon ministan harkokin wajen kasar Frank-Walter Steinmeier a matsayin sabon shugaban kasar Jamus da babban rinjaye,
wanda zai canji Shugaba Joachim Gauck.
Sabon shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier.

Sakamakon zaben da aka gudanar a ranar Lahadi 12 ga wannan wata na Fabarairu da muke ciki dai, ya nunar da cewa an zabi Frank-Walter Steinmeier da kuri'u 931 daga cikin 1.260 na 'yan majalisun da suka yi zaben, wadanda suka hada da 'yan majalisar tarayyar 630 da kuma 'yan majalisun jihohi 16 na kasar suma 630.

Shugaban kasa a Jamus dai ba shi da wani babban iko, amma kuma yana da kima sosai. Karfin ikon yana ga shugaban gwamnatin kasar da kuma majalisar dokoki. Sabon shugaban na Jamus Steinmeier ya samu goyon bayan jam'iyyarsa ta SPD, da kuma jam'iyyar shugabar gwmnatin ta Jamus din Angela Merkel.

tsohon shugan kasa a hannun hagu sai sabon shugaban kasa a hannun dama.


A watan Satumba ne dai za a yi zaben 'yan majalisar dokokin kasar inda Merkel ke neman wani sabon wa'adin mulki na hudu. Mukamin shugaban kasa a tarayyar Jamus matsayi ne da yake da kima sai dai a tsarin gudanar da mulki na kasar ba shi ne ke kan gaba ba wajen karfin fada a ji a kasar sabanin yadda yake a lokutan baya. Mafi akasari shugaban kasa a Jamus kan kasance ya nesanta kansa daga harkoki na siyasa wanda hakan ya sanya a ke kallon ofishinsa a matsayin wata alama ta hadin kan kasa.

Duk da cewar shugaban kasa kan wakilci kasar a kasashen ketare a wasu sabgogi da suka shafi Jamus, kana ya kan maida hankali wajen cigaban demokradiyar kasar da kuma tabbatarda mutunta dokokin da aka shimfida a kasar, bisa ga yadda dokokin kasar suka shimfida, wanda ke rike da mukamin shugaban gwamnati ne ke tafiyar da al'amura na yau da kullum na sha'anin mulki a kasar.

Amma dai a share guda shugaban kasa a Jamus kan kasance wanda ke sanya hannu a kan wasu yarjeniyoyi na kasa da kasa da suka shafi Jamus kuma shi ne ke sanya hannu kan wasu dokoki da majalisar dokokin kasar suka amince da su. Har ila yau shugaban kasa a Jamus kan tsoma baki kan wasu abubuwa da ke damun kasar da ma na wasu kasashen ketare ciki kuwa har da batun wanzar da zaman lafiya da hadin kan kasar da sauran kasashe da kuma batu da ya dangaci kare muhalli. Idan ya kasance an shiga rudani na siyasa a Jamus shugaban kasa shi ne ke da alhaki na gudanar da zabe musamman ma idan wanda ke rike da mukamin shugabar gwamnati ya rasa tudun dafawa a majalisar dokoki wato ya rasa rinjayen da ya kamata a ce ya na da shi, sai dai shugaban kasa a Jamus ba shi da karfin iko na saukewa ko nada ministoci ko alkalai ko kuma wasu manyan jami'an gwamnati kazalika ba ruwansa da batun da ya dangaci Jamus da wasu kasashe ta fuskar diflomasiyya musamman ma amincewa da jakadun kasashen waje ko akasin haka.

©facebook/HAUSAPOST28
No comments:
Write Comments