Tuesday

Home › › Tinubu Yayi bayani Akan Lafiyar Shugaba Buhari.
- Cif Bola Ahmed Tinubu yace wadanda basa cikin hankalinsu ne kawai ne zasuyi kokwanton ziyarar sa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a birnin Landan.
- Shugaban jam’iyyar ta APC na kasa baki daya yace abun bakin ciki ne a cewa wasu mutane na ta tada rikici a kan al’amarin hutun Buhari a birnin Landan .
- Tinubu yace hotunan da ya cika kafofin watsa labarai hujja ne na cewa shugaban kasar na nan cikin karfin sa.
- Tsohon gwamnan na jihar Lagas, ya bukaci yan Najeriya da su cire baki gurin kokarin tada rikici game da shugabanci da gwamnatin kasar .
Tsohon gwamnan jihar Lagas kuma shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC),
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, yace marasa hankali ne kawai zasu ce bai kasance tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari ba a Landan. A wani jawabi a ranar Litinin, wani tsohon gwamnan jihar Lagas, yace masu son tana rigima ne suke da alhakin yada labaran cewa bai ziyarci shugaban kasar ba. Jawabin dauke da sa hannun kakakin sa, Tunde Rahman, yace Tinubu ya kasance a birnin Landan tare da tsohon shugaban APC, Chief Bisi Akande, don ziyaran Buhari kuma sun hadu da shugaban kasa a gidan Abuja.


A wani al’amari makamancin wannan, Gwamna Ibikunle Amosun na jihar Ogun, ya tabbatar da cewa ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a Landan. Shugaban kasar na birnin Landan, yana samun kulawar likita kan wani cuta da ba’a bayyana ba. An samu rudani sosai kan wani hoto dake nuna Amosun da shugaban kasar a birnin Landan, wanda ake zargin cewa hoton tsoho ne aka sake wanke shi ya dawo sabo. Don haka, a ranar Litinin a gurin wani taro a Olusegun Obasanjo Presidential Library, Abeokuta, Amosun ya fada wa manema labarai cewa babu shakka ya ziyarci shugaban kasa a Landan.


©facebook/hausapost28
No comments:
Write Comments