Friday

Home › › Trump bai yi nasara ba a Kotun daukaka kara.
Harabar Kotun daukaka kara a San Francisco.Kotun daukaka kara a San Francisco ta tabbatar da yin watsi da dokar shugaba Donald Trump da ta haramtawa 'Yan gudun hijira da ‘yan kasashe bakwai na musulmi shiga Amurka. Alkalai uku na kotun daukaka karar ne suka amince da hukuncin da wata kotu a Seattle ta fara zartarwa na yin watsi da umurnin Trump wanda ya haramta shiga Amurka daga kasashe bakwai. Hakan na nufiin Donald Trump bai yi nasara ba bayan ya daukaka kara domin kalubalantar hukuncin kotun da ta fara yin watsi da umurnin shi.

Dokar Trump ta kunshi haramtawa ‘Yan gudun hijira shiga Amurka na tsawon kwanaki 120, tare da haramtawa ‘Yan kasashen Iran da Iraqi da Sudan da Syria da Somalia da Yemen na tsawon Wata uku.

Gwamnatin Trump dai na cewa daukar matakin wajibi ne saboda dalilai na tsaro domin kare Amurka daga mayaka irinsu IS da Al Qaeda. Amma matakin ya janyo suka daga ciki da wajen Amurka, inda wasu ke ganin gwamnatin Trump na kyamar musulmi ne wanda kuma ya sabawa dokokin kasar.
@facebook/HAUSAPOST28
No comments:
Write Comments