Wednesday

Home › › Uwar gidan marigayi "yar aduwa Ta bukaci ayiwa shugaba muhd buhari addu'a
Sakon Hajiya Turai 'Yar 'aduwa ga 'yan
Najeriya.Hajiya Turai 'Yar 'aduwa ta bayyana
hakan ne a shafinta na facebook, inda
ta shawarci 'Yan Nijeriya da fadin
alkari akan Shugaban da kaucewa furta
munanan kalamai.


Shi kuwa Aliyu Tilde cewa yayi Allah ya
bai wa Shugaban Kasa koshin lafiya, ya
yafe masa kurakuransa da
Zunubbanshi, ya shirye shi wajen
shugabantar lamurranmu.
Shugaba a ko’ina abinda ya cancanta
shi ne fada masa gaskiya a inda ake
ganin ya yi kure; addu’ar shiriyar
Ubangiji wajen shugabanci, da koshin
lafiya da gafarar Allah.
A wani labarin kuma, Ministan watsa
labarai, Lai Mohammed yace wannan
gwamnati ba ta da wata shiri na boye
ko ko a zahiri domin mai da kasa
Najeriya kasar musulunci kawai.
Lai mohammed ya fadi hakanne a taron
tattaunawa da mutane da akayi a garin
Ilori, jihar Kwara.
Lai Mohammed ya ce wannan zancen
kanzon kurege ne kawai domin babu
irin wannan magana ko mai kama
dashi lissafin wannan gwamnati.
Ya kara da cewa ‘yan siyasa ne kawai
suke amfani da irin wadannan kalamai
domin ingiza mutane da tada zaune
tsaye a kasa Najeriya.

@ Facebook.com/HAUSAPOST28
No comments:
Write Comments