Friday

Home › › Wannan muguwar Cutar Ta Kara Dawowa : LASSA
Wannan mugun cutar da aka sani na
‘Lassa’ ya dawo gari.

Yanzu haka ya hallaka mutane a Garin
Bauchi.

Kwamishinar lafiya ta Jihar ta bayyana
haka.

Wannan mugun ciwon ya kara dawowa Najeriya
‘Lassa’ mugun cutar nan da aka sani ta
dawo gari yanzu haka har ta aika wasu
bayin Allah Lahira.
Kamar dai yadda
aka sani dabbobi irin su bera ne ke
kawo zazzabin na Lassa.

Kamar yadda muka samu labari daga
jaridar Daily Trust, wannan mugun cuta
ta dawo Garin Bauchi har kuma tayi
sanadiyar mutuwar mutane 4.

Kwamishinar lafiya ta Jihar bauchi
Dakta Halima Mukaddas ta bayyanawa
manema labarai wannan a yau.

Dakta Halima tace an samu bullowar
cutar ne a Garuruwan Alkeri da
Ganjuwa. Kwanakin baya dai wannan
zazzabi na lassa ya bullo gari inda yayi
sanadiyar rashin rayukan mutane
kusan 2 a Bauchi. An dai gargadi Jama’a
su guji bera wanda shi ke yada kwayar
cutar.

A wani bangare kuma Masana masu
hange da binciken Duniya sun bayyana
cewa za a samu husufin rana a sassan
kasar nan a Ranar Lahadi. Ko da yake
dai masanan sun ce abin ba wani mai
kamarin gaske bane musamman a
Arewacin kasar.hausapost28 on Facebook
No comments:
Write Comments