Wednesday

Home › › Wata mata ta yi karar mijinta A kotu saboda fitsarin Kwance
A ranar Talatan nan ne dai wata matar
aure mai suna Blessing Ilo ta maka mijinta
a wata kotu dake garin Abuja saboda
tuhumarsa da takeyi akan aikata zina
da’yar cikinsa da take zama tare dasu.
Blessing ta fada wa kotu cewa mijinta na
lalata da yarinyar ne wanda ‘yar shekara
12 ne kacal a duk lokacin da ta fita zuwa
wajen aiki.


imageKo da yake ba itace mahaifiyar yarinyar
ba mijin nata ya gaya mata cewa
tsohuwar matarsa ce ta haifeta.
‘Yarinyar ta taba sanar da ‘yan sanda
cewa mahaifin nata na daure mata
hannaye kafin ya yi lalata da ita tun a
baya.

Blessing ta sanar wa kotu cewa dole ta
tattara inata-inata ta bar gidan domin
mijin ta mashayin giya ne na gaske.

Tace idan ya sha giyarsa ya bugu yakan
yi mata fitsari a gadonsu na kwanciya,
ko kuma a tsakar daki ko cikin randar
ruwan da suke sha. Sannan baya ciyar
da ita da dan da ta haifa masa sannan
baya biyan kudin makarantar dan.

Blessing ta roki kotun da ta raba
aurenta da shi mijin nata kuma ta bata
ikon rike dan da suka haifa.
Alkalin kotun Jemilu Jega ya ce kotu ta
kai wa mijin Blessing sammace har sau
uku amma ya ki zuwa kotu don haka ya
daga shari’ar karan zuwa 9 ga watan
Faburairun 2017.


@facebook/HAUSAPOST28
No comments:
Write Comments