Monday

Home › › WATA SABUWA: ‘Yan Boko Haram sun kwace wani gari a jihar Yobe
Wasu mambobi kungiyar "yan tada
kayar baya na Boko Haram sun kwace
garin Sasawa, wani gari a jihar Yobe da
suka far masa bayan musayar wuta da
rundunar sojin Najeriya a ranar
Lahadi, 5 ga watan Febrairu.


Duk da cewa rundunar sojin Najeriya
bata tabbatar da wannan labari ba,
wani rahoton jaridar Daily Post tace
yan ta’addan sun far ma garin da ke da
kilomita 30 daga babban birnin garin
Damaturu, a motoci da Babura.

Duk da cewar an fatattaki "yan ta’addan
daga dajin Sambisa, har yanzu basu
gushe suna kai farmaki garuruwan
mutane a yankin arewa maso gabas ba.

Rahoton ya ji maganganu daga
bakin mutanen garin wadanda suka
tabbatar da cewa yan ta’addan sun far
ma garin da yammacin ranan Lahadi
kuma sun fatattaki sojin nigeria.

Wani mazaunin garin yace a Damaturu
yace : “Mazauna sun arce domin neman
kariya yayinda yan ta’adda suna tayar
da bama-bamai kuma suna harbin kan
mai uwa da wabi.”


Rahoton ya tabbatar DA cewa an tura rundunar sojin
Najeriya zuwa garin yanzu.

muna nan:@fb.com/hausapost28/#
No comments:
Write Comments