Friday

Home › › Ya kashe ''"yan sanda bayan ya yaudare su
Jami’ai a arewa maso gabashin Afghanistan sun ce wani da ake kyautata zaton mayakin kungiyarTaliban ne, ya kashe a kalla ‘yan sanda takwas, ‘yan kwanaki bayan da ya yi saranda, ya shiga aikin dan sanda.

Kisan da aka yi a cikin dare ya auku ne a wani wurin binciken tsaro dake yankin Almar a lardin Fayrab.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na yankin Karim Yorosh ya shaidawa VOA yau juma’a cewa, maharin ya kwashe dukkan makamai da albarusai kafin ya gudu daga ofishin. Yace galiblin wadanda aka kashe sun fito daga zuriya daya ne.
Ance mayakin Taliban din ya yi saranda ga rundunar ‘yan sandan yankin ne kwanaki goma sha biyar da suka shige, ya kuma koma cikin mayakan bayan kai harin .

kasance damu @ HAUSAPOST28
No comments:
Write Comments