Monday

Home › › Yadda Obasanjo da Jonathan suka yaudari ‘yan Arewa | Farfesa Ango

Farfesa Ango Abdullahi ya ce zai yi wuya a nan gada yan arewa su yadda da wata yarjejeniya ta siyasa - Shugaban ya ce Obasanjo da Jonathan sun yaudari arewacin kasar Farfesa Ango Abdullahi Dandalin dattijon Arewa sun koka akan cewa tsohon shugabanin kasa Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan sun yaudari Arewa da kokarin bijirewa da tsarin karba-karba da aka amince da a jam’iyyar PDP.

prof- Ango-Abdullahi.


A cikin wata hira da jaridar SUN, Farfesa Ango Abdullahi ya ce jam’iyyar PDP ta amince da tsarin karba-karban shugabancin tsakanin Kudu da Arewacin kasar. Amma Obasanjo ya kaurace wa tsarin a yayin da ya nema shugabancin a karo na uku, kuma Jonathan bai cancanci ya tsaya takara a shekara 2015 ba, saboda arewa ya kamata ta gabatar da dan takara a lokacin.

Ya ce a lokacin da jam’iyyar PDP ke shawaran mulkin karba-karba a baya, wasu ‘yan jam’iyyar sun yi tir da tsarin musanma marigayi Abubakar Rimi wanda ya ce ya kamata a ba duk mai son takara dama. Amma mafi yawa sun bada goyon bayan tsarin karba-karba wanda ta ba kudanci dama ta gudanar da dan takara.

Wannan shi ya sa Obasanjo da Ekwueme suka kara a zaben, Obasanjo kuma ya lashe zabe. Obasanjo ya samu tikitin takara na biyu bayan wa’adin mulkin sa inda kuma ya lashe zabe.

Amma Obasanjo bayan shekaru takwas a mulki zai ya zama gagare a inda ya fito da wata dabara na neman wa’adi na uku a mulki wadda ta saba wa dokan kasa. Zai ya yi watsi da tsarin karba-karba ta jam'iyyarsa.

Ya yi kokari ya sa mutane su yi aiki domin wa'adi na uku, amma abin mamaki wasu daga cikinsu da yawa 'yan Arewa ne. Godiya ga Allah, a karkashin jagorancin marigayi Olusola Saraki kuma karkashin kungiyar addin kai arewa wadda nike mataimakinsa, mun hada karfin saboda mu yaki wannan al’amari kuma munci galaba a kan sa.

©facebook/HAUSAPOST28
No comments:
Write Comments