Saturday

Home › › ‘Yan Najeriya na kokawa kan yawan kudin da ake barna a kan shugaban kasa a Landan.‘Yan Najeriya sun fara kokawa kan
kudadin da ake kashe wa shugaban kasar
a yayin da yake hutun ganin likita a
Landan.

‘Yan Najeriya na kokawa kan yawan kudin da
ake barna a kan shugaban kasa a Landan
Jama’a na kiran gwamnatin tarayya
wajen inganta al'umma ta kiwon lafiya,
da kuma tsarin samar da kayayakin aiki
wadda ta dace da kiwon lafiya da kuma
yawon shakatawa.


Ana zato cewa shugaba Muhammadu
Buhari na biyan kudi caji tsakanin £200
da £250 a kowace awa, domin kula da
shi a kasar Ingila.

A cikin binciken jaridar Guardian, ta
bayyana cewa wadannan cajin kudin
asibiti na asibitoci masu zaman kansu
ne kawai a Birtaniya.
Wannan ya sanya mutane da yawa 'yan
Najeriya ke kokawa a kan
almubazaranci da fadar shugaban kasa
ke yi da dukiyoyin al’umma.


Gwamnati na kyautan na'ura ga ‘yan Nijeriya, yadda
za ka iya samu naka
Wani likita a bangaren kiwon lafiya,
Dr. Laz Ude Eze ya rubuta wata
budaden wasika zuwa ga shugaban
kasar Muhammadu Buhari a ranar
Jumma’a, 17 ga watan Fabrairu a inda
yake kokawa kan matsalolin da kasar ke
fuskanta a bangaren kiwon lafiya, ya
kuma zargi tsarin shugaban kasa a kan
dalilin zuwa Landan ganin likita bayan
zamu iya karfafa namu kiwon lafiya.
Ziyarar sauran jami’in gwamnati zuwa
ganin shugaban kasa a London kamar
IGP, Shugaban Majalisar Dattawa,
Kakakin Majalisar Dokoki , da dai
sauransu, duk a cikin dukiyar jama’a
Najeriya ne. Wadannan almubazaranci
ke kara durkushe tattalin arzikin kasar,
yayin da kuma talakawa ke cikin
tsananin rayuwa.


Dr. Laz ya ce:”Ban taba zato shugaban
kasa zai nema kiwon lafiya a kasashen
waje kamar magabata. A nawa gani
canjin da ka yi muna alkawari shine
zaka inganta asibitin fadar shugaban
kasa wadda za iya kula da lafiyar
shugaban kasa ba tare da zuwa kasan
waje ba.


HAUSAPOST28 on Facebook
No comments:
Write Comments