Saturday

Home › › "YAN SANDA SUN HANA ZANGA ZANGAR DA MAWAKI 2FACE YA SHIRYA A LAGOS DA ABUJA
Rundunar ‘yan Sanda a Najeriya ta haramta zanga-zangan nuna kyamar Gwamnati da wani mawaki ya shirya yi gobe lahadi da jibi Littini a biranen Lagos da Abuja.


Kakakin Rundunar ‘yan sandan Jimoh Moshood ya fadi cikin wata sanarwa cewa sun sami bayanan sirri dake nuna zanga-zangan nuna kyamar Gwamnatin Muhammadu Buhari da mawakin Innocent Idibia da aka fi sani da TuFace zai jagoranta akwai hadari.
Shi dai wannan mawaki ya sanar da shirya zanga-zangan ne saboda Gwamnatin yanzu ta ki yin komi gameda halin matsi da ake fama dashi.
Kungiyoyin dake rajin kare democradiyya dai sun nuna za su shiga wannan zanga-zanga a fadin kasar.
A cewar Rundunar ‘yan sanda akwai wasu rahotanni dake nuna wata kungiya na shirya nata zanga-zangan don nuna goyon bayan Gwamnati a lokacin da wanda TuFace ya shirya na si.
Wasu kafofin yada labarai a Najeriya sun ce TuFace ya ce za su gudanar da zanga-zangan duk da gargadin da aka yi masu.


Kazan ce damu @fb.com/hausapost28
No comments:
Write Comments