Tuesday

Home Yanzu yanzu Sako Daga Fadar Uban kasa
Masu Cewa Osinbajo yafi Buhari iya
mulki rashin hankali ne - Fadar
Shugaban kasaFadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa duk
muhimman matakan da Mukaddashin
Shugaban Kasa, Femi Osinbajo ke dauka
kan Harkokin kasar nan sai ya tuntubi
Shugaba Muhammad Buhari.Fadar Shugaban kasa dai ta fitar da
wannan bayanin ne bayan ikirarin da
bangaren adawa ya yi kan cewa tun
bayan da Mataimakin Shugaban ya
karbi ragamar jagorancin kasar nan
abubuwa suka fara gyaruwa sabanin
tsawon lokacin da Buhari ya yi kan
mulki.

Fadar ta shugaban kasar ta kuma ce
tabbas babban rashin hankali
maganganun da wasu mutanen da basu
son ci gaban kasar nan keyi na cewa
wai mukaddashin shugaban Kasa
Muhammadu Buhari watau Osinbajo
yafi shugaban iya mulki.
No comments:
Write Comments