Wednesday

Home › › YANZU-YANZU : Saraki, Dogara sun tafi Landan domin ganin Buhari
Saraki, Dogara, Lasun, Lawan sun tafi Landan domin ganin Buhari

Shugaban majalisar dattawa, Dr. Bukola Saraki, ya jagoranci wata tawagar mutane 4 domin kaiwa shugaba Muhammadu Buhari ziyara birnin Landan.

Sauran mambobin tawagar sune kakakin majalisan wakilai, Yakubu Dogara, mataimakin kakakin majalisa, Lasun Yusuf da shugaban masu rinjayen majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan.

Tawagar sun tafi Landan ne ranan Laraba da safe domin gaishe shugaba Buhari wanda ya tsawaita ranan dawowarsa saboda jinyan da yakeyi a birnin Landan. Tashar Channels tace majiya a majalisar dokoki ta tabbatar mata da hakan.


http://fb.com/HAUSAPOST28
No comments:
Write Comments