Tuesday

Home Za a fara zuwa yawon bude ido duniyar wata : Yanzu haka fasinjoji sun gama biyan kudin su.

Bayan shekaru 45 a karon farko kamfanin SpaceX na Amurka zai aika wasu 'yan yawon bude ido zuwa duniyar wata.Bayan shekaru 45 a karon farko kamfanin SpaceX na Amurka zai aika wasu 'yan yawon bude ido zuwa duniyar wata.

Za a tura mutanen su 2 a shekarar 2018 wadanda aka ki a bayyana sunayensu.

Shugaban kamfanin na SpaceX Elon Musk ya bayyana cewa, sun karbi kudade daga hannun fasinjojin da za su tura amma bai fadi ko nawa ba ne.

A wannan shekarar za a fara duba lafiyar mutanen tare da ba su horo wadanda za su je duniyar ta wata bayan shekaru 45 da aka dauka babu wanda ya je.
No comments:
Write Comments