Monday

Home A Yau Litinin Buhari Zai Ziyarci Dajin Sabimsa Don Bude Gasar Sojoji.
A yau Litinin ne ake sa ran shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari zai ziyarci dajin nan na Sambisa da ke jihar Borno wanda kuma a baya ya kasance babbar helkwatar mayakan kunigyar Boko Haram don bude gasar nuna kwarewar sarrafa kananan makamai tsakanin sojojin kasar.

A kwanakin baya ne dai babban kwamandan horarwa da tsare-tsare na rundunar sojin Nijeriyan Manjo Janar David Amadu ya sanar da hakan inda ya ce a yayin gasar na bana dai sojojin za su gwada irin kwarewar da suke da ita musamman wajen tattaro bayanai da kuma gwada wasu makamai da suke da su.

Ana sa ran Ministan tsaro na Nijeriyan Alhaji Mansur Dan Ali, babban hafsan hafsoshin kasar Janar Gabriel Olanisakin, babban hafsan sojojin kasa Laftanar Janar Tukur Buratai, babban hafsan sojojin sama Air Vice Marshal Abubakar Sadique , babban hafsan sojojin ruwa Vice Admiral Obet Ebas da sauran manyan hafsoshin sojin Nijeriya su ne za su rufa wa shugaba Buharin baya.

A watan Disamban bara ne dai sojojin Nijeriya suka yi nasarar fatattakar ‘yan Boko Haram daga Dajin na Sambisa bayan rike shi na shekara da shekaru.
No comments:
Write Comments