Sunday

Home Abin da Gwamna Fayose Yace gameda dawowar Buhari
Gwamna Fayose yace shugaba Buhari na da aiki a gaban sa.

Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Peter Fayose ya kira ‘Yan Najeriya su cigaba da yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’a domin ya samu sauki. Gwamnan yace akwai aiki na gyaran kasar a gaban shugaba Buhari.

Ayo Fayose yayi wannan magana ne kamar yadda muka samu labari a wajen ta’aziyyar tsohon Gwamnan Yamma Janar Adeyinka Adebayo a Birnin Ado-Ekiti. Fayose yace kowa ya damu game da rashin lafiyar shugaban kasar don haka a taya sa da addu’a.

KU KARANTA: Nan gaba PDP zata iya mulki na tsawon shekaru 60. : General Babangida

Fayose yayi addu’a Ubangiji ya ba shugaban kasar karfin tafiyar da mulkin yace domin yana bukatar gyara abubuwa da dama da suka tabarbare a kasar. Duk da haka dai Fayose yace za suyi ta addu’a Buhari ya sauko da farashin dala zuwa N200 sannan kuma samu saukin abinci.No comments:
Write Comments