Wednesday

Home › › Abin Harda bokaye? : Hukumar EFCC ta gurfanar da boka akan damfarar N5.6millionHukumar Hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta gurfanar da wani boka mai suna Clement Joseph alias Dr. Omale a ranan Talata.

An gurfanar da Clement Joseph alias Dr. Omale ne a babban kotun birnin tarayya Abuja da me zaune a Lugbe Abuja.

Yana fuskantar laifuka 7 na damfaran Judi N5.6 miliyan
Harda bokaye? Hukumar EFCC ta gurfanar da boka akan damfarar N5.6million.

A ranan Talata, 7 ga watan Maris, Hukumar Hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta gurfanar da wani boka mai suna Clement Joseph alias Dr. Omale gaban alkali Jastis A. Otaluka.

Game da cewa kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, bokan na fuskantar laifuka 7 wanda ya kunshi yaudara da damfaran na kudi N5.6 million.

KARANTA WANNAN :- Chakwakiya: Ya Auri Kanwarsa A Auren Zawarawan Da Ya Gabata A Kano

Shi da abokan yaudaran shi wadanda suka arce sun damfari wani mai suna Bola Akintola da sunan cewa zasu tsiratar da ita daga mutuwan fuji'a.


Jawabin yace:

“ Clement Joseph (Alias Dr. Omale), Mr. Paul , Mr. Papa , Mr. Ifeanyi da Mrs Ments a ranan 26 ga watan Yunin 2016 sun amshi kudi miliyan 1 daga hannun Mrs Bola Akintola akan cewa ku bokaye ne kuma kun amshi kudin domin tsubbu na hanata mutuwan fuji'a.

Alkali Jastis Otaluka ya dakatad da karar zuwa ranan 23 ga watan Maris domin fara ainihin gurfana.

No comments:
Write Comments