Thursday

Home An cafke wani daga cikin mayakan boko haram a garin bauchi
AN CAFKE WANI KWAMANDAN KUNGIYAR BOKO HARAM A TITIN AHMADU BELLO DAKE CIKIN GARIN BAUCHI
Jami’an tsaron farin kaya a jihar Bauchi, sun sami nasarar cafke daya daga cikin kwamandojin kungiyar Boko Haram, mai suna Nasiru Sani, wanda ake wa lakabi da Osama.

An cafke kwamandanne a titin Ahmadu Bello, dake cikin garin Bauchi, ‘yan kwanaki kadan da suka gabata, kamar yadda wata sanarwa da jami’an tsaron farin kaya ta SSS, ta aiko mana ta nuna cewa Osama, na daya daga cikin kwamandojin ‘yan kungiyar Boko Haram da aka taba kamawa amma ya tsere daga gidan fursuna na garin Bauchi, a watan Oktoba na shekarar 2010.

Shima babban dan kungiyar ta Boko Haram, mai suna Adamu Jibrin, da ya saje da jama’a har ya canza suna zuwa Dantata Sule, yake kuma kai komo tsakanin manyan kwamandojin kungiyar da mayakan, an cafke shi a kasuwar Jeka da Fari, a garin Gombe, tare da mai gidansa da ake kira Kananbu.

Hukumar tsaron farin kaya ta SSS, ta bayyana cewa daga watan jiya zuwa wannan da muke ciki, ta kama kusoshin kungiyar da dama a jihohin Bauchi, Yobe, Kaduna,Gombe, Nasarawa da Kogi.

Shugaban hukumar wayar da kan jama’a NOA, Dr Garba Abari, ya ce wannan fafatawa bata jami’an tsaro kadai bace.
Hukumar ta SSS, ta bada sanarwar kama wani dillalin kungiyar mai suna Usman Ladan Rawa, da ya kamawa Abdullahi Isa hayar gida a Lafiya, dake jihar Nasarawa, inda suka shirya domin zuwa kaddamar da hare harensu a birnin tarayya Abuja da Minna, da kuma sauran jihohin dake tsakiya Najeriya.
No comments:
Write Comments