Saturday

Home AN KAMA MOTAR KAMFANIN DANGOTE DAUKE DA TABAR WIWI A JIHAR EDOHukumar dake kula da fataucin miyagun kwayoyi wato NDLEA dake reshen jihar Edo ta kama wasu mutane uku dake dauke da tabar wiwi.

Hukumar tace tabar wiwin da jami’an NDLEA suka kama takai darajar zunzurutun kudi kimanin Miliyan N183
Jami’an da sukayi nasarar kama wannan mota sun shaidawa manema labarai cewa mafi yawancin motar duk tabar wiwi ce,sai kuma wasu buhun siminti da akasa a matsayin basaja domin batar da lissafin ma’aikatan tsaro dake kan hanya
Hukumar tace abisa kokarin wadannan direban dake dauke da wannan tabar wiwi ya nuna cewa suna kokarin shigar da ita ne zuwa jihar Maiduguri Borno State.

Direban ya fadawa hukamar ta NDLEA ainihin cikakken Sunan sa kamar haka Zegiru Amadu
A wata tattaunawa da wani kwamanda hukumar fataucin miyagun kwayoyi dake Edo Mista wakawa Buba yace wannan tabar wiwi tanada hadarin gaske fiye da kowa tabar wiwi sannan kuma yace yana yabawa kungiyar Operation 3 data jajirce wajen zurfafa bincike wajen kama wannan mota dake dauke da wannan tabar wiwi
Zegiru Amadu Direban motar yace an biya sa kudi kimanin Naira miliyan N1.3 domin ya kai tabar wiwin zuwa jihar Borno.
No comments:
Write Comments