Saturday

Home An Kashe Mutane Fiye Da 50 A harin Da Aka Kai wa Kauyuka Uku : Afirka Ta Tsakiya.
An zargi mayakan Silka ne da kai hari a cikin kauyukan uku wanda ya ci rayuka fiye da 50.

Kauyukan da hare-haren su ka shafa dai sune Agoudou-Manga, Yesseneme da Ngouyanza a tsakiyar kasar.

Majisar dinkin duniya da kungiyoyin agaji sun bayyana takaicinsu akan sake dawowar tashe-tashen hankula a cikin kasar ta Afirka ta tsakiya. Bugu da kari, kungiyoyin sun bayyana matsalolin da su ke fuskanta na karacin kudaden da za su taimakawa wadanda su ke da bukatuwa da taimako a cikin kasar.

Kusan rabin al'ummar kasar ra Afrika ta tsakiya ne dai su ke da bukatuwa da taimako.

Tare da cewa an sami koma bayar ricike-rikicen da kasar ta ke fama da shi, sai dai duk haka yana ci gaba da bullo kai daga lokaci zuwa lokaci.
No comments:
Write Comments