Monday

Home › › An saki mawakin nan na jihar Kano, Sadiq Zazzabi

Kotu ta bada umurnin sakin mawakin jihar Kanon nan wanda yayi wakan yabon Kwankwaso, Sadiq Zazzabi akan beli.

An gurfanar da Zazzabi akan cewa ya saki wata waka akan tsohon gwamna, Rabiu Kwankwaso, ba tare bin ka’idar cibiyar sakin wakoki da bidiyo ba.
A yau Litinin, an bashi belin akan sharuuda 3: Kudi N100,000, wani mamaban kungiyar marubutan wakan jihar Kano, da kuma wani ma’aikacin gwamnati wanda ya kai akalla matsayi na 14.


Ya cika sharuddan belin kuma an sake shi kuma an dakatad da karar zuwa ranan 27 ga watan Maris. Zazzabi yace an tsareshi ne saboda cewa shi masoyi tsohon gwamna Kwankwaso ne.
Injiniya Kwankwaso da gwamna mai ci, Abdullahi Ganduje sun kasance cikin sa’insa kuma mabiyansu na rikici isu-isu.
Yayinda yake Magana da jaridar Premium Times, shugaban hukumar, Ismaila Afakallahu, ya tabbatar da cewa an sake shi.
No comments:
Write Comments