Friday

Home Ango ya kori amarya washegarin biki : Auren Zawarawa Na kano
Fusataccen ango ya kori
amaryarsa washegarin auren
zawarawa da akayi a Kano.Habiba Inusa ta kasance daya daga cikin
wadanda suka amfana daga auren zawarawa a
jihar Kano wanda aka gudanar a ranar
Lahadi, 26 ga watan Fabrairu. Ta yi
nasarar boye cikin ta daga mijin nata
sannan ta haihu washegarin auren.


Daily Nigerian ta ruwaito cewa Habiba
ta shiga nakuda washegarin auren
sannan ta haifi da namiji. Wannan ya
sa mazauna yankin Gangare na
karamar hukumar Doguwa cikin jimami
a matsayinsu na wadanda suka shirya
bikin.

Angon Habiiba, Babangida ya kori ta da
yaron daga gida saboda ba shine yayi
mata cikin ba.

Ml. Aminu Daurawa, kwamandan hukumar
Hisbah ta Kano, yace an tantance
ma’auratan sosai, kuma anyi masu
gwaje-gwajen lafiya da sauran abubuwa
kafin auren.

Lokacin da aka nemi yayi magana kan
al’amarin Habiba, yace: “An bukaci mu
kawo sunayen ma’aurata watanni
shidda bayan mun tantance su a
hukumar kiwon lafiya ingantacce na
ma’aikatar lafiya. Gwamnati ta yanke
shawarar barin kananan hukumomi
rikon al’amarin. Don haka komai na iya
faruwa.”

No comments:
Write Comments