Sunday

Home Ba zan iya tuna lokacin karshe da aka sanya min jini ba. : SHUGABA BUHARI
Shugabna kasa Muhammadu Buhari ya ce ba zai iya tuna lokacin karshe da aka sanya masa jini ba.

Shugaban kasar ya kara da cewa babban kalubalen da ke fuskantar tsarin kiwon lafiyar Najeriya shine kula da kai
Akwai alamomin cewa an sanya ma shugaban kasa Muhammadu Buhari jini a yayinda yake kasar Ingila kan kula da lafiyar sa.

A yayin da shugaban kasar ke magana da manyan jami’an gwamnati a ranar Juma’a, 10 ga watan Maris bayan dawowar sa ya ce ba zai iya tuna lokaci na karshe da aka sanya masa jini ba a rayuwar sa, jaridar Punch ta ruwaito cewa,

Yayin da yake magana kan kalubalen da ya fuskanta a lokacin hutun sa shugaban kasa Buhari ya ce: “Ba zan iya tuna lokaci na karshe da aka sanya mun jini ba; gaskiya ba zan iya tuna wa ba, zan dai iya cewa a cikin shekara ta na 70.”

Yayinda shugaban kasar ya bayyana babban kalubalan da ke fuskantar tsarin lafiyar Najeriya, bai dai ce kowannan bane ya yi sanadiyan rashin lafiyar da yayi ba.


Ya ce: “Ina ganin daya daga cikin muggan abubuwa shine shan magani da kai. Bamu yarda da likitocin mu ba sannan mun fi yarda da kawunan mu.”
“Inda na ziyarta, sukan sha magani ne idan akwai bukatar yin haka. Ba sa hadiyan komai da komai,”
inji Buhari.
“Na samu lafiya sosai a yanzu; babu mamaki akwai bukatar wasu abubuwa da zasu biyo baya a cikin wasu makonni,” cewar sa.

Ya ci gaba da yaba ma mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo kan kokarinsa gurin kula da al’amuran kasar yayinda ya tafi hutu.

KU KARANTA KUMA: WAKAR RARARA NEW (BARKA DA ZUWA BABA BUHARI) : up dated

A halin yanzu, shugaban kasa Buhari ya shawarci yan Najeriya da su tsaya a inda suke don yi masa da Najeriya addu’a a maimakon zuwa Abuja don yi masa sannu da zuwa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya a ranar Juma’a, 10 ga watan Maris, bayan hutun ganin likita a kasar Ingila.

A lokacin da yayi tafiya, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo yayi aiki a matsayin mukaddashin shugaban kasar Najeriya.


No comments:
Write Comments