Wednesday

Home Ba zan taba ja da Buhari a takaran shugabancin Najeriya ba – Inji Bola Ahmed Tinubu


Tsohon gwamnan jihar Legas Bola Ahmed Tinubu yace ba zai ja ba ko yayi takaran shugabancin kasa Najeriya da Buhari kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka fadi.
Gidan jaridar THIS DAY ta rubuta wata labari cewa wai Tinubu na shirin fitowa takaran shugabancin kasa a 2019.

Tinubu yace wannan labarin da gidan jaridar ThisDay ta rubuta bai kamata ba saboda bashi da niyyar fitowa takaran shugabancin kasa Najeriya.
Bayan haka kuma gidan jaridar ta ce Tinubu na nazarin canza sheka zuwa jam’iyyar PDP in da ya musanta hakan itama.

Tunde Rahman da ya sanya hannu ga wannan martani da Tinubu yayi akan rahoton ThisDay din ya ce duk wanda ya san Tinubu zai san mutum ne mai tsatssauran ra’ayin da ba zai dauki irin wannan shawara ba ko mataki ba.

Ya kuma ce Tinubu ba zai canza jam’iyysa ba saboda yana daya daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar APC sannan kuma yana daya daga cikin mutanen da suka tabbatar cewa an kubutar da ‘yan Najeriya daga cikin kangin jam’iyyar PDP ta saka su.
Rahman ya ce dalilin da ya sa wannan gidan jaridar ta rubuta labarin shine domin ta kirkiro wata kiyayya a tsakanin Tinubu da shugaban kasa Muhammadu Buhari amma yana tabbatar wa mutane cewa hakan ba zai taba yiwuwa ba saboda ko shugaban kasa na kasan ko ba ya nan goyan bayansa ga Buhari ba zai taba canza wa ba.

Daga karshe Tinubu yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari fatan Allah ya bashi Lafiya ya kuma dawo mana da shi gida lafiya.
No comments:
Write Comments