Friday

Home Gwamnatin Shugaba Buhari Zata Gina Gidaje 180,000 kyauta Ga talakawa.
An kammala shirin gina ma talakawa gidaje
180,000 kyauta a Najeriya - Daraktan ANDPWata kungiya mai zaman kanta mai suna
Kungiyar samar da cigaba a nahiyar Afirka,
ANDP zata gina gidaje guda 180,000 a fadin
kasar nan da zata raba ma talakawa kyauta ba
ko sisi.

Gidajen za’a gina su ne masu dakuna biyu biyu,
kuma za’a watsa sune a shiyoyi daban daban na
dukkanin jihohin, sa’annan za’a gina musu
makarantu, ofishin yansanda, kasuwanni da
asibitoci.

Wannan kungiya ta ANDP wani sashi ne na tsarin
cigaban duniya ta bayyana cewa zata raba
gidajen ne ga talakawa kyauta, daraktan kungiyar
mai suna Samson Omojuyigbe ya shaida ma
kamfanin dillancin labaru, NAN cewa gidajen zasu
lakume zambar kudi naira triliyan 2.8, sa’annan
yace za’a gina gidajen ne guda 5000 a kowane
jiha a kan naira biliyan 78.

Samson yace: “ANDP wata kungiya ce mai zaman
kanta, kuma zata kashe makudan kudade wajen
samar ma jama’an Afirka gidaje kyauta, musamman
wadanda suke cikin halin matsin tattalin arziki.
Mun gwammace mu gina ma talakawa gidaje
kyauta, akan mu dinga kai kayyayin tallafi sansanin
yan gudun hijira ana cinyewa.

“Zamu gina gidaje ciki biyu biyu har guda 5000 a
kowane jiha na kasar Najeriya, abinda ya bamu
kwarin gwiwar shigowa mu tallaha shine yadda
gwamnatoci a kowane mataki suke fama da
karancin kudi da ba zasu iya magance matsalolin
jama’a gaba daya ba.

“Wannan ne yasa muka hada kai da kungiyoyi
masu zaman kansu, tare da masu hannu da shuni
don ceton al’umma ta hanyar sama musu rayuwa
mai inganci. Ko sisin kobo gwamnati ba zata kashe
a wannan harkar ba, face goyon baya da muke
bukatar su bamu don samun nasarar aikin. Burin
kungiyar mu kawai shine kawar da talauci daga
nahiyar Afirka.”


Dayake bayani kan yadda za’a raba gidajen,
Samson yace: “Ba zamu samu matsala wajen
rabon gidajen ba, za muyi amfani da ilimin kimiyya
wajen fitar da wadanda suka cancanci a basu
gidajen ba tare da da nuna fifiko ga wani ko wasu
ba, ba zamu yarda da sa bakin kowa ba a harkar
rabon gidajen, saboda muna sa ran mutane su
nuna tsoron Allah."


Mista Samson yace a yanzu haka jihohin Enugu,
Ebonyi, Akwa Ibom da Kross Ribas sun bayar da
filayen da za’ayi gine ginen, inda yace tuni an
kaddamar da fara aikin gine ginen a kauyen Ikpa
Nkanya na garin Kros Ribas akan wani katafaren
fili eka 250 wanda gwamnatin jihar ta bayar.
Samson ya cigaba da fadin jihohin Kaduna, Kano,
Jigawa da Adamawa sun yi alkawarin bayar da
nasu filayen nan bada dadewa ba.
No comments:
Write Comments