Thursday

Home Gwamnonin APC zasu yi wata ganawa mai muhimmanci a AbujaDukkan illahirin gwamnoni 24 da aka zaba
a APC za suyi wata ganawa mai
muhimmacin gaske a Abuja yau din nan
tare da bangaren zartarwa na jam'iyyar.Majiyar mu ta LEADERSHIP ta bankado
kuma cewa muhimman bayanan da za'a
tattauna a taron sune yadda za'a
gudanar da babban gangamin jam'iyyar
da kuma harkar kasafin kudin bana.

A wani labarin kuma, Hukumar da ke
kula da harkokin mai ta kasa watau
Nigerian National Petroleum
Corporation (NNPC) a jiya ta sanar da
rufe babbar matatar mai dake garin
Wari.

Hukumar ta Nigerian National
Petroleum Corporation (NNPC) tace
hakan ya zama dole ne saboda wasu
yan gyare gyare da za'a yi da kuma
wasu matsalolin da suka taso.

Shugaban matataun mai na NNPC din
Mr. Anibor Kragha ne ya bayyana haka
a Abuja inda kuma yace yanzu haka dai
matatun man dake Fatakwal da Kaduna
ne kawai ke aiki.
No comments:
Write Comments