Wednesday

Home Halin da tsohon shugaban Kasar Gambia ya shiga bayan ya tsere daga karagar mulkin kasarTsohon shugaban Gambia, Yahaya Jammeh ya
koma gona


Tsohon shugaban kasar Gambia Yahaya Jammeh
wanda a yanzu yake gudun hijira a kasar
Equatorial Guinea ya rungumi harkar noma
gadan gadan, inda aka hange shi a cikin gona.

Dama dai tun bayan komawarsa kasar Equatorial
Guinea, Jammeh ya bayyana cewar shifa yanzu
harkar noma zai koma ba kama hannun yaro,
tunda dai Duniya tayi mai darasi.

Kamar yadda rahoton jaridar BBC ya nuna,
Jammeh ya kammala shirye shiryen fara harkar
noman, sai dai ba’a tabbatar da wani irin noman
zai shiga yi ba, amma dai hotunansa sun bayyana
a cikin wata katuwar gona.

Idan ba’a manta ba, Jammeh ya tsere daga kasar
Gambia ne bayan wani bore da yan kasa suka yi
masa a daidai lokacin dayaki sauka daga mulki
bayan ya sha kayi a zabukan kasar, duk da cewa
ya kwashe shekaru 22 yana mulki.

Tserewar da yayi ne ya baiwa zababben
shugaban kasar Adama Barrow daman darewa
kujerar mulki, bayan kungiyar kasashen Afirka na
yamma sun matsa ma Jammeh lamba.

HOTUNANo comments:
Write Comments