Tuesday

Home Hukumar EFCC Ta Damke Wani Shehin MalamiHukumar EFCC mai yaki da cin hanci a Najeriya ta kama wani mai suna Sheikh Saheed Omoniyi a Garin Ibadan bisa ga laifin zamba


EFCC mai yaki da cin hanci a Najeriya tayi ram da wani mai suna Sheikh Saheed Omoniyi bisa ga laifin zamba cikin aminci inda yake cutar mutane a yanar gizo da sunan cewa shi malami ne na Allah.

Wani Jami’in EFCC na Yankin Kudu ya bayyana haka ga manema labarai a Yau Alhamis. Ayo Oyewole yace Mista Omoniyi mai shekaru 24 ya saba damfarar mutane tun ba yau ba.

Matashin yana yaudarar Jama’a da cewa shine babban Malamin nan na Legas Sheikh Sulaiman Onikijipa.

KU KARANTA: Tambayoyi Hudu Da Dan Aljanna Ne Kadai Zai iya bada Amsarsu

An dai gano cewa wannan matashi yayi sama da kudin Jama’a har fiye da Naira Miliyan 11 inda yake fakewa da sunan wani Babban Shehi, An damke wannan mutumi ne yayin da yake hanyar zuwa Bankin bayan ya damfari wani.

No comments:
Write Comments