Friday

Home › › Hukumar INEC ta Bayyana Ranakun zaben 2019

Hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta alanta ranan 16 ga watan Fabrairu a matsayin ranan da za’a gudanar da zaben shugaban kasan 2019.
Kwamishanan INEC na yankin kudu maso yamma, Solomon Soyebi, ya bayar da wannan sanarwan ne a wata hira a yau Alhamis, 9 ga watan Maris a Abuja.

Kana kuma Soyobi ya bayyana cewa hukumar zata gudanar zaben gwamnoni- majalisar dokokin jiha da a Abuja a ranan Asabar, 2 ga watan 2019.


KARANTA WANNAN : "Shugaba Buhari zai dawo Yau Juma’a" – Femi Adesina

Wani sashen jawabin yace: “ A Najeriya, kundin tattalin arzikin Najeriya ta bada tsarin cewa a gudanar da zabe akalla saura kwanaki 30 kafin karewar wa’addin gwamnatinsa. Domin tabbatar da kwanankin zabe da kuma shiri na kwarai ga hukumar, jam’iyyun siyasa, jami’an tsaro, masu takara, da masu ruwa da tsaki, hukumar ta yanke shawaran sanya ranan gudanar da zabe a mako na 3 a watan Fabrairu, sannan na gwamnoni mako biyu nag aba. Sabod haka, za’a gudanar da zaben shugaban kasa da majalisan dokokin tarayya ranan asabar, 16 ga watan Fabrairu 2019, sannan a gudanar da na gwamnoni, majalisun dokokin jiha, da birnin tarayya ranan asabar, 2 ga watan Maris, 2019.

A bangare guda, an nemi hukumar INEC tayi dubi cikin dokar INEC kafin a gudanar da zaben 2019. Wani gangamin jam’iyyun siyasa 25 ne sukayi wannan bukata a ranan Laraba, 8 ga watan Maris.No comments:
Write Comments