Thursday

Home "Ina a masallaci lokacin da majalisa ta dakatar da ni" : sanata ali Ndume

Sanata Muhammad Ali Ndume wanda majalisar
dattawan Najeriya ta dakatar, ya ce ya tafi
sallah a lokacin da majalisar ta dakatar da shi.
Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa yana
masallaci lokacin da majalisa ta dakatar da shi.

A ranar Laraba ne dai kwamitin da'a na Majalisar
dattawan kasar ta dakatar da sanata Ali Ndume
bisa dalilin rashin cikakken bincike kafin gabatar
da korafi.

NAIJ.com ta ruwaito cewa shi dai sanata Ali
Ndume ya nemi da zauren majalisar ya yi bincike
kan wasu labarai da jaridun kasar suka buga
dangane da zarge-zarge kan shugaban Majalisa,
sanata Bukola Saraki da sanata Dino Melaye.
Jaridun dai sun nuna cewa shugaban Majalisa,
sanata Bukola Saraki matsa wa shugaban
hukumar Kwastam, Hameed Ali, lamba ne saboda
jami'an hukumar sun kama motar da ya shiga da
ita kasar ba tare da biyan kudin haraji ba.
Shi kuma sanata Dino Melaye, jaridun sun nuna
shakku kan kammala digirinsa daga jami'ar
Ahmadu Bello da ke Zaria.

To amma bayan wanke shugaban majalisar da
sanata Dino Melaye daga zarge-zargen, kwamitin
da'a na majalisar ta dattawa ta zartar da
hukuncin dakatar da sanata Muhammad Ali
Ndume daga majalisar na tsawon watanni shida.
No comments:
Write Comments